Ƙasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso sun miƙa takardar haɗin gwiwa ta neman karɓar baƙuncin gasar cin Kofin Nahiyar Afirka, AFCON, ta shekarar 2032.

Jami'an ƙasashen uku sun gabatar da takardar buƙatar ga Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF), Patrice Motsepe.

Ganawar ta gudana ne a birnin New York na Amurka, inda shugabannin hukumomin ƙwallon ƙafa na ƙasashen uku suka halarta tare da Kanar Djibrilla Hima Hamidou, wakilin Nijar a Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA).

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Mali (FEMAFOOT) ta sanar da wannan mataki a ranar Talata, tana mai cewa manufar neman karɓar baƙuncin ita ce ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashen yankin da kuma bunƙasa harkar ƙwallon ƙafa a nahiyar Afirka.

Hukumar ta ƙara da cewa za ta yi aiki tare da Nijar da Burkina Faso wajen shirya ingantaccen tsari na karɓar baƙuncin gasar, idan aka ba su damar gudanar da ita.

Har yanzu Hukumar CAF ba ta zaɓi ƙasar ko ƙasashen da za su karɓi baƙuncin gasar AFCON ta shekarar 2032 ba.

Matakin ya zo ne bayan ƙasashen uku, waɗanda ke ƙarƙashin Ƙungiyar Ƙasashen Sahel (AES), sun nuna sha'awarsu ta haɗa kai wajen gudanar da manyan ayyukan ci gaba, ciki har da wasanni, baya ga haɗin gwiwarsu a fannonin tsaro, kasuwanci da tattalin arziƙi.