Wata kotu a Ghana ta yanke wa wani matashi mai shekara 26, Ebenezer Frimpong, hukuncin ɗaurin wata ɗaya a gidan yari bayan samunsa da laifin yunƙurin satar motar 'yan sanda.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a watan Afrilu lokacin da matashin ya shiga wata motar sulke ta 'yan sanda tare da fara tafiya da ita, bayan direban motar, Joshua Denkyi, ya tsaya a wani kantin sayar da magunguna domin saye.
Direban motar ya bayyana cewa matashin ya yi amfani da damar da ya samu yayin da ya fita daga motar, inda ya yi ƙoƙarin guduwa da ita.
Sai dai jami'an 'yan sanda sun bi motar tare da kama matashin kafin ya samu nasarar tserewa.
Kafin yanke hukunci, alƙalin kotun ya ba da umarnin a gudanar wa matashin gwajin lafiyar ƙwaƙwalwa domin tabbatar da cewa yana cikin cikakken hankalinsa.
Bayan Ebenezer Frimpong ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin wata ɗaya a gidan yari.
Alƙalin ya bayyana cewa ya rage tsawon hukuncin ne saboda wanda ake tuhumar ya amsa laifinsa tun da farko, lamarin da ya taimaka wajen gaggauta kammala shari'ar.