Gwamnatin Tarayya ta gargadi jama'a da su guji taɓa wata farar kumfa da ta bayyana a gefen babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, bayan zargin cewa wata mota mai ɗaukar kaya ta zubar da wani sinadari a wurin.

Hukumar Kula da Ka'idojin Muhalli ta Ƙasa (NESREA) ta ce ta fara bincike domin gano musabbabin samuwar kumfar da kuma tabbatar da ko tana da haɗari ga lafiyar jama'a ko muhalli.

A cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Yaɗa Labarai ta hukumar, Nwamaka Ejiofor, ta fitar, an ce jami'an NESREA daga ofishin Kaduna sun ziyarci wurin domin gudanar da bincike.

Sanarwar ta ce tawagar ta gana da Kwamandan 'Yan Sanda na Jere, ACP Sani Zubairu, da jami'an Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), tare da shugabannin al'ummar yankin domin tattara bayanai kan lamarin.

Binciken farko ya nuna cewa wata babbar mota ce ta yi hatsari a wurin, lamarin da ya jawo zubar da kayan da take ɗauke da su.

NESREA ta ce ta tattara bayanai daga jami'an gwamnati da mazauna yankin, sannan ta ɗauki samfurin kumfar, ƙasar wurin da kuma ruwan wani rafi da ke kusa domin gudanar da gwaje-gwajen dakin bincike.

Hukumar ta yi kira ga jama'a da su guji kusantar kumfar, ruwan da ke kusa da wurin da kuma ƙasar da ke kewaye da shi har sai an kammala binciken, domin kauce wa duk wata barazana ga lafiya ko muhalli.