Farashin ɗanyen mai na ci gaba da ƙaruwa a kasuwannin duniya yayin da rikici ke ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya.

A yau Talata, farashin mai ya ƙaru da kusan kashi biyu cikin ɗari, inda ya kai matakin da ba a gani ba cikin makonni biyar.

Rahotanni sun nuna cewa farashin ɗanyen man Brent ya haura dala 92 kan kowace ganga, yayin da na West Texas Intermediate, wato WTI, ya haura dala 84 kan ganga.

Masana sun danganta wannan hauhawar farashi da fargabar yiwuwar tangarɗa ga samar da makamashi daga yankin Gabas ta Tsakiya, sakamakon rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran, da kuma barazanar da mayakan Houthi na Yemen suka yi kan hanyoyin jigilar mai zuwa Saudiyya.

Sai dai Hukumar Kula da Makamashi ta Duniya (IEA) ta bayyana cewa duk da ƙarin fargabar da sabon rikicin ya haifar, har yanzu kasuwar makamashi ta duniya na da ƙarfin da za ta iya jure wa duk wani matsin lamba na ɗan lokaci.

Shugaban hukumar, Fatih Birol, ya ce ƙara tsanantar rikicin da ya shafi mashigin Hormuz da cibiyoyin samar da makamashi a yankin ya ƙara haifar da rashin tabbas game da makomar kasuwar ɗanyen mai ta duniya.