Kakakin Majalisar Wakilan Tarayya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa Majalisar ta samar da wani tsari na musamman da ke da nufin ƙara bai wa mata damar shiga harkokin siyasa da kuma tsayawa takara a Najeriya.
Abbas ya ce sabon tsarin zai bambanta da yadda ake gudanar da tsarin takara ga sauran ’yan siyasa, inda za a fara aiwatar da shi a matsayin gwaji na wasu shekaru kafin a tantance tasirinsa da yadda ya dace da tsarin siyasar ƙasar.
Ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin Majalisar na inganta wakilcin mata a matakan shugabanci da kuma ƙarfafa shigarsu cikin harkokin siyasa.
A wani ɓangare na jawabinsa, Kakakin Majalisar ya musanta zargin da ke cewa Majalisar Wakilan Tarayya ta zama mai bin umarnin Shugaban Ƙasa ba tare da yin nazari ba.
A cewarsa, Majalisar tana gudanar da ayyukanta ne cikin cikakken ‘yancin kai, bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, tare da sanya muradun al’ummar ƙasa a gaba wajen yanke duk wani hukunci.