Tsohon Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya yi nasara a zaɓen fidda gwani na Sanatan Delta North, inda ya doke Sanata mai ci Ned Nwoko. Okowa ya samu ƙuri'u 113,309, yayin da Nwoko ya samu ƙuri'u 2,612 a zaɓen da Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta gudanar. A mazaɓar Sanatan Delta ta Tsakiya.

Zaɓen fidda gwani wanda aka gudanar bisa tsarin Option a duk kananan hukumomi takwas na mazaɓar, ya sami halartar mambobin jam'iyyar da yawa kuma an bayyana shi a matsayin lumana, ingantacce kuma bayyananne.