Arsenal na dab da lashe gasar Firimiyar Ingila, karo na farko cikin shekaru 22, bayan da ta doke Burnley a karawarsu ta daren jiya, da ci ɗaya mai ban haushi.
Karawar da Arsenal ta yi a daren jiya ita ce wasanta na ƙarshe a gida a gasar Firimiya, kuma nasarar da ta samu ta ƙara matsa wa Manchester City lamba a wasan da za ta yi da Bournemouth a daren yau.
Kafin fara wasan, magoya bayan Arsenal sun gudanar da ƙwarya-ƙwaryar biki a filin wasa na Emirate, inda suka ɗaga tutoci da ke nuna farin cikin da suke ciki. A yanzu haka, Arsenal ta haɗa maki 82, inda take da tazarar maki 5 a kan City. Suna fatan City ta zubar da maki a wasanta na yau, domin ta samu damar lashe gasar kai tsaye ba tare da ta jira nasara a karawarta ta ƙarshe da Crystal Palace ba.