Mace mafi ƙanƙanta a duniya wacce ke yawo da taimakon keken guragu mai sarrafa kansa, Wildine Aumoithe, ta kafa tarihi wajen samar da damammaki a guraben da babu wanda ya taɓa samu. A tsawonta da ya kai inci 2 ft 4 ko kuma 72cm, ita ce mace mafi gajarta a fannin kwararriya mai tallan kayan ƙawa a duniya. Sai dai waɗannan bajinta da ta lashe guda biyu na Guiness World Record suna ne da suka karaɗe kafafen watsa labarai. Ainihi labarin shi ne yadda take amfani da su. An haife ta kuma ta girma a birnin Miami na Amurka ga iyayenta ‘yan asalin Haiti, Wildine tana da cutar SADDAN dysplasia, wani nau'in cutar gajarta wanda ya sa a mafi yawan lokuta take tafiya da taimakon keken guragu. Bayan an haife ta a 2003, likitoci ba su yi zaton za ta iya rayuwa a bayan wannan daren ba. 'Mutum, mutum ne, komai ƙanƙantarsa' Fast forward almost 23 years, and she is not just surviving; she is thriving and making sure other people feel seen. Ga shi har ta kai shekaru 23, kuma ba wai kawai rayuwa take yi ba ; tana ci gaba tare da ba wasu mutanen dama.
Back to News