Oyo State ta gargadi mazauna jihar da masu sayar da dabbobi da su guji sayar da shanu da raguna a manyan tituna yayin bikin Eid al-Adha mai zuwa.

Bayanin hakan ya fito ne yayin taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da dokar hana kiwo a fili ta shekarar 2019 da aka gudanar a Ibadan, kamar yadda Jaridar PUNCH ta rawaito.

Gwamnatin ta bayyana cewa dokar ba ta nufin nuna wariya ga wata ƙabila, tana mai cewa an tanadi kasuwannin sayar da dabbobi a dukkan ƙananan hukumomin jihar domin gudanar da kasuwanci cikin tsari.

Shugabar Hukumar Tabbatar da Bin Doka ta jihar, Aderonke Aderemi, ta ce duk wanda aka kama yana sayar da dabbobi a manyan tituna zai fuskanci hukunci, tare da ƙwace dabbobin da aka kama.

Ta ce an kafa dokar ne domin rage rikicin manoma da makiyaya, kare gonaki, da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar. Gwamnatin ta kuma buƙaci haɗin kan jami’an tsaro, shugabannin al’umma, manoma da makiyaya wajen tabbatar da bin dokar