cikin wata sanarwa da Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a madadin Shugaban Hukumar Abba Elmustafha Mai dauke da kawanan watan 16 ga watan mayu 2026, ya bayyana cewa hukumar ta dakatar da Amina Uba Hassan da Adam Garba bayan samun su cikin wannan bidiyo daya sabawa tarbiya.

Abdullahi Ya ƙara da cewa, dakatarwar na nufin an hana su gudanar da duk wani aikin fim a Jihar Kano har tsawon shekara guda.

Abdullahi ya kuma bayyana cewa dokar hukumar ta bai wa hukumar ikon dakatar da duk wani ɗan masana’antar Kannywood daga gudanar da harkokin fim a Kano, kuma karya wannan doka na iya jawo hukunci mai tsauri a ƙarƙashin doka.

Da yake jawabi a yayin dakatarwar, Shugaban Hukumar, Abba El-Mustapha, ya ja hankalin ’yan masana’antar Kannywood da su guji duk wani abu da ka iya zubar musu da mutunci ko kawo rashin kima ga masana’antarsu