Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Hukumar Kula da Gogayya da Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kayayyaki ta Nijeriya (FCCPC) da ta gudanar da bincike kan manyan kamfanonin fasaha, ciki har da Meta, Alphabet (Google), X da wasu kamfanonin da ke haɓaka fasahar kirkirarriyar basira (AI), bisa zargin amfani da dabarun hana gogayya da kuma anfani da labaran kafafen yaɗa labaran Nijeriya ba tare da bin ƙa'ida ba.

A wata sanarwa da FCCPC ta fitar, ta ce matakin ya biyo bayan wata takardar ƙorafi da Ƙungiyar Kamfanonin Yaɗa Labarai ta Nijeriya (NPO) ta shigar. Ƙungiyar na wakiltar manyan kamfanonin kafafen yaɗa labarai a faɗin ƙasar.

Sanarwar ta bayyana cewa hukumar za ta binciki ko ayyukan kamfanonin sun saɓa wa tanade-tanaden Dokar Kare Gogayya ta Kasuwanci da Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kayayyaki (FCCPA) ta shekarar 2018 ko wasu dokoki masu alaƙa da hakan.

FCCPC ta ce binciken zai kasance mai zaman kansa, cikin gaskiya da adalci, kuma zai dogara ne da hujjoji. Haka kuma, ta jaddada cewa za a bai wa dukkan ɓangarorin da abin ya shafa damar kare kansu, inda ta bayyana cewa ba a riga an yanke hukunci kan zarge-zargen ba.

Hukumar ta ƙara da cewa manufar binciken ita ce tabbatar da daidaito tsakanin bunƙasar fasaha da kuma kare martaba da dorewar kafafen yaɗa labarai, waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya.

Wannan mataki ya yi kama da abin da aka ɗauka a Afirka ta Kudu, inda Google ya amince da wani shiri na tallafawa kafafen yaɗa labarai na ƙasar bayan makamancin koke da aka shigar. Sai dai har yanzu ba a bayyana cewa za a ɗauki irin wannan mataki a Nijeriya ba.