Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ƙasarsa na da ƙarfin da za ta iya murƙushe Iran cikin ƙanƙanin lokaci, amma ya ce ya fi son a warware rikicin ta hanyar tattaunawa da cimma yarjejeniya.

A wata hira da ya yi da talabijin, Trump ya ce farashin mai bai yi tashin gwauron zabi ba duk da matsalolin da suka shafi mashigin ruwa na Hormuz, yana mai cewa Amurka ta ci gaba da samun isasshen mai.

Trump ya kuma yi iƙirarin cewa hare-haren da Amurka ta kai sun lalata jiragen ruwan yaƙin Iran, jiragen saman rundunar sojin saman ƙasar da kuma tsarin na'urorin rada, lamarin da ya ba wa dakarun Amurka damar kai hare-hare cikin sauƙi.

Haka kuma ya ce rundunar ruwan Amurka ta kakaba wa Iran ƙaƙƙarfan takunkumi ta hanyar ƙawance tashoshin jiragen ruwanta na tsawon watanni biyu, kafin daga bisani a sassauta matakan domin bai wa tattaunawa damar gudana.

Trump ya ce Amurka za ta cimma manufarta ta kowace hanya, ko dai ta hanyar yarjejeniya ko kuma ta amfani da ƙarfi.

“Za mu iya murƙushe Iran cikin ƙanƙanin lokaci, amma na fi son a cimma yarjejeniya saboda ba na son miliyoyin mutane su sha wahala,” in ji shi.

Ya kuma yi barazanar cewa Amurka na da ikon rusa gadoji da cibiyoyin samar da wutar lantarki na Iran cikin ɗan lokaci idan rikicin ya ƙara tsananta.

Sai dai waɗannan kalamai na Trump iƙirari ne daga gare shi, kuma ba a samu wani tabbaci mai zaman kansa da ke tabbatar da dukkan ikirarinsa ba. Har ila yau, hukumomin Iran ba su fitar da wata sanarwa da ta mayar da martani kan waɗannan kalamai ba.