Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ƙara jefa kanta cikin abin kunya da shakku a idon jama’a, bisa abin da ya bayyana a matsayin ƙoƙarin kare Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, daga zarge-zargen da suka shafi Hukumar PFIPC.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce bayanan da ke cikin Dokar Kasafin Kuɗin 2026 sun nuna abin da ya kira karkatar da manufar kasafin kuɗi, inda aka ware biliyoyin naira domin ayyukan gina hanyoyi a ƙarƙashin Hukumar Kula da Almajirai da Yaran da Ba sa Makaranta, duk da cewa irin waɗannan ayyuka ba sa cikin nauyin da doka ta ɗora wa hukumar.
Ya bayyana cewa an ware kusan naira biliyan 1.4 domin gyara da gina hanyoyi a Jihar Ogun, sannan aka sake ware wata biliyan 1.4 domin ƙarin ayyukan hanyoyi a wasu yankuna. Haka kuma, an ware biliyan 1.05 sau biyu domin wasu ayyukan hanyoyi, abin da ya ce ya saba da manufar kafa hukumar.
Atiku ya ce abin mamaki ne yadda aka mayar da hukumar da aka kafa domin kula da ilimin yaran da ba sa makaranta tamkar hukumar gina hanyoyi, yana mai cewa hakan na nuna an karkatar da kasafin kuɗi tare da yin watsi da matsalar sama da yara miliyan 20 da ke wajen makaranta a Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi zargin gwamnatin APC da amfani da ƙananan hukumomi wajen ɓoye ayyukan da ake cece-kuce a kansu domin rage yiwuwar binciken jama’a da kuma sauƙaƙa karkatar da kuɗaɗen gwamnati.
Ya tunatar da cewa a kasafin kuɗin shekarar 2023 ma an yi zargin karkatar da kuɗaɗen da aka ware wa Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Umunze, Jihar Anambra, zuwa ayyukan mazaba a Surulere, Jihar Legas, lokacin da Femi Gbajabiamila yake Kakakin Majalisar Wakilai.
Dangane da zarge-zargen da suka shafi Hukumar PFIPC, Atiku ya ce gwamnatin tarayya ba za ta iya kawar da batun da musanta wa kawai ba. Ya yi nuni da zargin da Prince Adeniyi Adeyemi ya yi cewa an buƙaci ya biya naira miliyan 400 a gaba tare da kusan rabin tallafin fara aikin hukumar da ya kai naira biliyan 27.4 domin tabbatar masa da mukamin Darakta Janar.
Har ila yau, Atiku ya tambayi dalilin da ya sa har yanzu ba a gurfanar da Adeyemi a kotu ba idan da gaske gwamnati na kallonsa a matsayin mai damfara. Ya kuma yi tambaya kan yadda har yanzu yake gudanar da ayyukansa daga Sakatariyar Tarayya da kuma yadda ya samu damar kai ziyara ga shugabannin EFCC duk da kasancewar ana bincikensa.
A ƙarshe, Atiku ya ce Shugaba Tinubu ba zai iya cewa bai san abin da ke faruwa ba, domin Dokar Kasafin Kuɗin 2026 tana ɗauke da sa hannunsa. A cewarsa, idan shugaban ya amince da waɗannan abubuwa, hakan na nuna haɗin kai wajen aikata ba daidai ba, idan kuma bai sani ba, hakan na nuna gazawar sa ido kan yadda ake tafiyar da gwamnati.
Lura: Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, gwamnatin tarayya da Femi Gbajabiamila ba su fitar da wata sanarwa da ke mayar da martani kan waɗannan sabbin zarge-zarge ba.