Jam'iyyar ADC a Kano ta sauke shugabanninta tare da naɗa Umar Bala Umar Kwalwa a matsayin sabon shugaban riƙo.
"Ɗan Takarar Gwamnan ADC a Kano Na Tallata Asiwaju Bola Ahmed Tinubu" — Naja'atu Bala Muhammad
Hajiya Naja'atu Bala Muhammad ta zargi ɗan takarar gwamnan jam'iyyar ADC a Jihar Kano da cewa yana fi mayar da hankali wajen tallata Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu maimakon ya yi aikin bunƙasa da tallata jam'iyyarsa ta ADC.
Ta bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano, inda ta sanar da sauke shugabannin jam'iyyar ADC na jihar tare da naɗa sabbin shugabannin riƙo da za su jagoranci harkokin jam'iyyar har zuwa lokacin da za a kammala sake fasalin shugabancinta.
A cewarta, matakin da aka ɗauka ya zama dole domin farfaɗo da jam'iyyar, ƙarfafa tsarinta, da kuma tabbatar da ingantaccen shugabanci wanda zai haɗa kan mambobi tare da shirya jam'iyyar domin fuskantar zaɓuɓɓuka masu zuwa.
Naja'atu Bala Muhammad ta jaddada cewa sabbin shugabannin riƙon za su gudanar da ayyukansu cikin adalci da gaskiya, tare da tabbatar da cewa an sake gina jam'iyyar bisa tsari mai ƙarfi da zai amfani mambobinta a Jihar Kano.