Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta sanar da ƙara wa'adin ci gaba da rajistar masu zaɓe na tsawon makonni biyu domin bai wa ƙarin ƴan Najeriya da suka cancanta damar yin rajista kafin babban zaɓen 2027.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Hukumar, Mohammed Kudu Haruna, ya sanya wa hannu, INEC ta ce ta ɗauki matakin ne bayan nazarin yadda aikin rajistar ke gudana da kuma la'akari da shawarwarin da ta samu daga ofisoshinta na jihohi, jam'iyyun siyasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki.

Hukumar ta bayyana cewa aikin rajistar, wanda ya fara a ranar 18 ga Agustan 2025 kuma aka tsara kammala shi a ranar 10 ga Yulin 2026, yanzu zai ci gaba har zuwa ranar Lahadi, 26 ga Yulin 2026.

INEC ta kuma sanar da ƙaddamar da sabon tsarin rajistar masu zaɓe ta yanar gizo ga waɗanda ke yin rajista karo na farko.

A cewar hukumar, daga ranar 8 ga Yulin 2026, masu neman yin rajista za su iya shiga shafin intanet na INEC domin cike bayanansu kafin su kammala sauran matakan rajistar a hukumance.

Hukumar ta buƙaci duk masu cancantar yin rajista da su yi amfani da wannan ƙarin wa'adi domin tabbatar da sun samu katin zaɓensu kafin wa'adin ya ƙare.