Rahotanni sun nuna cewa an dakatar da shirin ne bayan tattaunawa da jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki kan yiwuwar tasirin sa ga harkokin siyasa da tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.


Mashigar Hormuz na da muhimmanci matuƙa ga kasuwancin man fetur na duniya, kuma duk wata matsala a yankin kan haifar da tashin farashin mai da fargaba a kasuwannin duniya.


Matakin na Trump ya zo ne a lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan tsaro da zaman lafiya a yankin Gulf, musamman dangane da hulɗar Amurka da Iran