Shugaban Rasha, Vladimir Putin, zai kai ziyara ƙasar China daga ranar 19 zuwa 20 ga watan Mayu, kwanaki kaɗan bayan ziyarar da shugaban Amurka Donald Trump ya kai Beijing.

Fadar Kremlin ta bayyana cewa Putin zai gana da shugaban China, Xi Jinping, domin tattauna yadda za a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da alaƙar dabarun siyasa da tattalin arziki tsakanin Moscow da Beijing.

Sanarwar ta ce shugabannin biyu za su tattauna muhimman batutuwan duniya da na yankuna tare da sanya hannu kan wata sanarwar haɗin gwiwa bayan ganawarsu.

Haka kuma ana sa ran Putin zai gana da firaministan China, Li Qiang, domin tattauna batutuwan tattalin arziki da kasuwanci.

Sanarwar ziyarar Putin na zuwa ne bayan Trump ya kammala wata muhimmiyar ziyara a China, wadda ita ce ta farko da shugaban Amurka ya kai can cikin kusan shekaru goma.

Duk da kyakkyawar tarbar da aka yi wa Trump, har yanzu akwai manyan saɓani tsakanin Amurka da China, ciki har da batun yaƙin Ukraine da Rasha.

China dai na ci gaba da kira da a tattauna domin kawo ƙarshen yaƙin, amma ba ta taɓa Allah wadai da matakin Rasha na tura sojoji Ukraine a shekarar 2022 ba.

Beijing kuma na musanta zargin cewa tana bai wa Rasha makamai ko kayan yaƙi, tana mai cewa ƙasashen Yamma ne ke tsawaita rikicin ta hanyar bai wa Ukraine tallafin makamai.