Ƙungiyar Likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta yi gargaɗin cewa matsalar tamowa na ci gaba da barazana ga rayuwar dubban yara a jihar Kebbi da ma yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, inda ta ce ana samun ƙaruwar yara masu fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana cewa alƙaluman da ta tattara sun nuna ƙaruwa mai yawa a yawan yara masu fama da tamowa tsakanin shekarun 2024 da 2025, lamarin da ya tilasta mata sauya dabarun agaji domin dakile matsalar kafin ta ƙara muni.
MSF ta ce bayanan Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) sun nuna cewa kusan yara 30 cikin 100 masu ƙasa da shekara biyar na rasa rayukansu a kullum sakamakon matsalolin da ke da alaƙa da tamowa, yayin da kusan rabin waɗannan mace-mace ke faruwa ne a jihar Kebbi.
Shugaban MSF a Najeriya, Stuart Alexander Zimble, ya bayyana cewa rashin abinci mai gina jiki ya zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa mutuwar jarirai da ƙananan yara a jihar.
Ya ce abin damuwa ne yadda yara da dama da a baya ke fama da matsakaicin tamowa yanzu ke shiga mawuyacin hali, wanda ke ƙara jefa rayuwarsu cikin haɗari.
Ƙungiyar ta kuma danganta taɓarɓarewar lamarin da ƙarancin rigakafi da kuma yawaitar cutar zazzabin cizon sauro, waɗanda ke ƙara raunana lafiyar yara.
Domin rage matsalar, MSF ta ce ta fara amfani da wani tsarin ciyarwa mai suna "Tom Brown", wanda aka tsara domin taimaka wa yara masu fama da tamowa da kuma hana matsalar ƙara tsananta.