Najeriya da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari Ta Yuro Miliyan 365
Kasashen Najeriya da Jamus sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta yuro miliyan 365 domin bunkasa tattalin arziki, makamashi, noma da kuma ci gaban bangaren masu zaman kansu.
Yarjejeniyar na da nufin karfafa zuba jari na dogon lokaci tare da inganta ci gaban tattalin arziki da samar da damammaki a fannoni daban-daban na kasar