Bayanai daga hukumar kula da albarkatun man fetur ta Nijeriya NMDPRA sun nuna cewa an samu ragi a adadin danyen man fetur da kasar ke shigowa da shi daga ketare cikin watan Afrilun 2026.

Bayanan sun nuna cewa cikin ganga miliyan 18.37 da aka rarrabawa matatun man cikin gida, ganga 410,000 ne kacal aka shigo da su daga waje, yayin da aka samar da miliyan 17.96 a cikin kasar, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito