Dangote Refinery ta fitar da jimillar lita biliyan 1.66 na man fetur da sauran dangogin mai a watan Afrilu 2026, a cewar sabbin bayanai daga Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA).

Rahoton ya nuna cewa an raba adadin ne zuwa lita miliyan 513 na fetur, lita miliyan 534 na dizal, da kuma lita miliyan 615 na man jiragen sama.

NMDPRA ta ce matatar, wadda ke da ƙarfin tace ganga 650,000 a rana a Lekki, Jihar Legas, ta yi aiki da kashi 99.12% na ƙarfin ta a watan Afrilu, inda ta kasance babbar matatar da ke samar da mai a Najeriya.

Rahoton ya ƙara da cewa matatar na samar da kusan lita miliyan 55.4 a kowace rana, tare da fitar da wani kaso zuwa ƙasashen waje duk da buƙatar cikin gida.

Masana harkar mai sun danganta ƙarin buƙata da rashin tabbas da rikicin Gabas ta Tsakiya, musamman tasirin rikicin United States da Iran kan tsaro a mashigar ruwan Strait of Hormuz.

Duk da ƙarin samar da mai a cikin gida, farashin fetur ya ci gaba da tashi a Najeriya, inda NMDPRA ta danganta hakan da hauhawar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.