Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da sabbin matakan da nufinsu shi ne ƙarfafa bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗen gwamnati da kuma inganta gaskiya da riƙon amana a ma’aikatun gwamnati.
A ƙarƙashin sabbin ƙa’idojin, an rage adadin kuɗaɗen gudanarwa da ake warewa ministoci domin ayyukan gaggawa da sauran buƙatun ofis zuwa Naira 700,000.
Matakin na daga cikin sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa domin tabbatar da an bi dokokin kuɗi yadda ya kamata tare da rage almubazzaranci a amfani da dukiyar jama’a.
Sabuwar ƙa’idar ta fito ne cikin wata takarda da ta tanadi iyakar kuɗaɗen da jami’an gwamnati za su iya kashewa ba tare da bin tsarin kwangila ba. Takardar, wadda Ministan Kuɗi ya amince da ita, Ofishin Akanta-Janar na Tarayya ne ya fitar a matsayin sanarwar hukuma.
Bisa ga tsarin, an kayyade kuɗaɗen da sakatarorin dindindin da shugabannin hukumomi za su iya kashewa zuwa Naira 500,000, yayin da daraktoci da shugabannin sassa za su iyakance zuwa Naira 300,000.
Haka kuma, shugabannin ofisoshi na jihohi da sauran masu riƙe da mukaman gwamnati za su iya kashe kuɗi har zuwa Naira 100,000 kacal a irin waɗannan lokuta.
Gwamnatin ta kuma jaddada cewa duk wata sayayya da ta haura Naira miliyan ɗaya dole ne a bi tsarin bayar da kwangila kamar yadda dokar saye da sayarwa ta gwamnati ta tanada.
Mahukunta sun bayyana cewa matakin zai taimaka wajen ƙarfafa gaskiya, rage almubazzaranci da kuma tabbatar da amfani da kuɗaɗen jama’a cikin tsari da adalci.