Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, Florentino Pérez, ya sake lashe zaɓen shugabancin ƙungiyar ba tare da hamayya ba, wanda hakan ya ba shi damar ci gaba da jagorantar kulob ɗin a karo na shida.
Pérez, mai shekaru 79, zai ci gaba da zama shugaban Real Madrid har zuwa shekarar 2030, bayan da babu wani ɗan takara da ya cika sharuddan tsayawa takara a zaɓen.
Tun bayan komawarsa shugabancin ƙungiyar a shekarar 2009, Pérez ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarori masu yawa, ciki har da lashe kofunan gasar zakarun nahiyar turai da dama da kuma bunƙasa tattalin arzikin kungiyar.
Magoya bayan Real Madrid na sa ran sabon wa’adin nasa zai ƙara ɗaga martabar ƙungiyar a matakin ƙwallon ƙafa na duniya.