United States ta sanar cewa za ta sassauta tsarin biyan kuɗin jinginar biza ga wasu magoya bayan tawagogin ƙasashen da za su halarci gasar cin kofin duniya.

A baya, a ƙarƙashin manufofin tsohon shugaban ƙasa Donald Trump na ƙara tsaurara shige da fice, an fara buƙatar wasu ‘yan ƙasashe su biya tsakanin $5,000 zuwa $15,000 a matsayin jingina kafin a ba su biza, kuɗin da ake mayarwa idan sun bi ƙa’ida suka koma ƙasashensu.

Sai dai Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce yanzu za a ɗauke wannan jingina ga magoya bayan da ke da tikitin shiga wasannin gasar cin kofin duniya da kuma waɗanda suka yi rajista a tsarin biza na musamman da aka tanada.

Ƙasashen Afirka biyar da ke cikin waɗanda suka samu tikitin shiga gasar — Algeria, Cape Verde, Ivory Coast, Senegal da Tunisia — suna daga cikin ƙasashen da matakin jinginar ya taɓa shafa.

Mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka, Mora Namdar, ta ce manufar su ita ce ƙarfafa tsaron ƙasa tare da tabbatar da tafiya bisa doka yayin shirye-shiryen gasar cin kofin duniya mai zuwa.