Tsohon sufeton ’yan sandan Najeriya, Usman Baba Alƙali, ya sanar da janyewarsa daga neman takarar Glgwamnan jihar Yobe.
Usman Baba Alƙali wanda ke neman takarar gwamnan Yobe a jam'iyyar APC, ya sanar da haka ne ta wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Ya bayyana cewa ya yanke shawarar janyewa ne domin tabbatar da samun haɗin kai da daidaito da kuma nasarar APC da kuma ci-gaban Jihar Yobe.
A cewarsa ya ɗauki matakin ne bayan ganawa da mataimakin shugaban Ƙasa Sanata Kashim Shettima da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum da kuma Gwamna Mai Mala Buni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a na jihar Yobe