Bankunan Nijeriya sun tara N209bn daga ladan kula da asusu cikin watanni ukun farkon shekarar 2026
Wasu sabbin bayanai da jaridar Punch ta tattaro sun nuna cewa bankunan Nijeriya sun tara Naira biliayan 209 daga kudaden da suke cira na kula da asusu (Account maintenance fees) cikin watanni uku na farkon shekarar 2026.
Hakan na nuna cewa an samu kari kan Naira biliyan 183 da suka samu a watanni ukun farkon shekarar 2025.