Hukumar kula da wutar lantarki ta Nijeriya, ta fara aiwatar da sabbin dokokin da za su bai wa masu amfani da solar damar sayar da wutar lantarkin da ta yi musu yawa ga kamfanonin rarraba lantarki.

Jaridar punch ta bayyana cewa sabon tsarin zai ƙarfafa amfani da makamashi musamman na hasken rana, tare da bai wa masu zuba jari a fannin samar da wuta damar samun ƙarin riba.

A ƙarƙashin sabon tsarin, masu amfani da solar za su fara amfani da wutar da suka samar domin bukatunsu, idan kuma an samu wutar fiye da abin da suke buƙata, za su iya tura wa ga kamfanin rarraba lantarki domin sayarwa.