Kyiv ta sake fuskantar wani gagarumin hari ta sama daga Russia, inda jami’an ceto ke ci gaba da laluben waɗanda lamarin ya rutsa da su a ƙarƙashin ɓaraguzai.
Magajin garin Kyiv, Vitaliy Klitschko, ya ce harin ya yi ajalin mutum biyu tare da jikkata kusan mutane 40. Ya bayyana cewa ginin da harin ya shafa ya ƙunshi ɗakuna 18, kuma lamarin ya lalata wasu hanyoyin samar da ruwa a birnin.
A ranar Laraba, Russia ta kai ɗaya daga cikin manyan hare-haren sama kan Ukraine tun bayan fara yaƙin tsakanin ƙasashen biyu.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya ce Moscow ta harba sama da jirage marasa matuƙa 800, yayin da jami’an ceto suka samu nasarar kuɓutar da mutane da dama daga gine-ginen da suka rushe.