Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Labour Party, Peter Obi ya ce idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa, zai yi wa’adi guda ɗaya ne kacal na shekaru huɗu, yana mai jaddada cewa ba zai wuce wa’adin ba “ko da an ɗora masa bindiga a kai.”

Obi ya bayyana hakan ne a cikin wata gajeren bidiyo daga wata hira da ake sa ran za a watsa a tashar News Central TV a ranar Alhamis.

Inda ya ce “Ina son zama shugaban ƙasa na wa’adi guda ɗaya saboda tabbatar da daidaito da kwanciyar hankali. Ba zan ƙara kwana ɗaya ba bayan shekaru huɗu, ko da an ɗora mini bindiga a kai,” in ji shi a cikin bidiyon da ke yawo