Jakadan Nijeriya a ƙasar Amurka, Kayode Are, ya fara aiki a hukumance bayan miƙa takardun kama aikinsa ga Shugaban Amurka, Donald Trump.

Gabatar da takardun kama aikin na daga cikin muhimman matakan diflomasiyya da ke tabbatar da fara aikin jakada a ƙasar da aka tura shi aiki.

Rahotanni sun bayyana cewa bikin ya gudana ne a wani taro na musamman da aka shirya a fadar shugaban ƙasar Amurka, inda aka karɓi sabbin jakadu daga ƙasashe daban-daban.