Tauraron matashin dan wasan Barcelona, Lamine Yamal, na cikin jerin ‘yan wasan da kocin Spain, Luis de la Fuente, ya bayyana domin gasar Kofin Duniya ta 2026 duk da cewa yana fama da rauni.
Kocin ya kuma saka dan wasan Arsenal, Mikel Merino, bayan dawowarsa daga jinya sakamakon karayar ƙafa da ta hana shi taka leda tun watan Janairu.
A karo na farko a tarihin Kofin Duniya, tawagar Spain ba ta kunshi ko dan wasa daya daga Real Madrid ba, bayan da aka cire Dean Huijsen da kuma Dani Carvajal wanda ya yi fama da raunuka a kakar wasa.
De la Fuente ya kuma gayyaci Eric Garcia da Marc Pubill bayan rawar da suka taka a Barcelona da Atletico Madrid, yayin da aka bar Huijsen da Robin Le Normand a waje.
Tare da Yamal mai shekaru 18, dan wasan Athletic Bilbao Nico Williams ma yana cikin tawagar duk da cewa ya yi fama da matsalolin rashin lafiya a kakar bana.
Sai dai akwai shakku kan ko Yamal zai buga wasannin farko na gasar bayan raunin tsoka da ya samu tare da Barcelona wanda ya hana shi taka leda tun karshen watan Afrilu.
Yamal na daya daga cikin ‘yan wasan Barcelona takwas da aka saka a tawagar tare da Pedri, Gavi da mai tsaron raga Joan Garcia.
Kocin Spain, Luis de la Fuente, ya ce suna aiki tare da likitocin kungiyoyin ‘yan wasan domin tabbatar da lafiyarsu kafin fara gasar.
Ya bayyana cewa rahotannin da suka samu sun nuna cewa dukkan ‘yan wasan za su kasance cikin shiri kafin wasan farko ko na biyu.
Dan wasan tsakiya Gavi ya dawo taka leda a watan Maris bayan doguwar jinya sakamakon mummunan raunin gwiwa, kuma ya nuna bajinta a wasannin karshen kakar bana tare da Barcelona.
Yamal ya wallafa wani bidiyo a shafukan sada zumunta inda aka nuna Gavi cikin farin ciki bayan sanar da sunansa cikin tawagar Spain.
Kocin ya ce wannan na nuna kyakkyawar alakar da ke tsakanin ‘yan wasan da kuma muhimmancin wakiltar kasar Spain.
Da aka tambaye shi kan rashin saka ‘yan wasan Real Madrid a tawagar, De la Fuente ya ce ba ya kallon kulob din da dan wasa yake bugawa kafin yanke hukunci.
Ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne dan wasan ya cancanci wakiltar kasar.
Spain za ta fara yakin neman kofin duniya ne ranar 15 ga Yuni da Cape Verde a rukunin H, kafin daga bisani ta kara da Saudiyya da Uruguay.
Tawagar Spain:
Masu tsaron raga:
Unai Simon, David Raya, Joan Garcia
Masu tsaron baya:
Marcos Llorente, Marc Pubill, Pedro Porro, Aymeric Laporte, Eric Garcia, Pau Cubarsi, Marc Cucurella, Alejandro Grimaldo
‘Yan wasan tsakiya:
Rodri, Martin Zubimendi, Mikel Merino, Pedri, Gavi, Fabian Ruiz, Alex Baena
‘Yan wasan gaba:
Yeremy Pino, Victor Munoz, Mikel Oyarzabal, Ferran Torres, Lamine Yamal, Dani Olmo, Nico Williams, Borja Iglesias