Hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya Federal Road Safety Corps ta shawarci direbobin da ke tafiya ta hanyar Abuja zuwa Kaduna da su yi amfani da wasu hanyoyi domin kauce wa cunkoson da ke addabar babban titin a wannan lokaci na bukukuwan Babbar Sallah.

Hukumar ta ce ana samun taruwar ababen hawa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna sakamakon yawan masu tafiya Sallah da kuma ayyukan gyaran hanya da ke gudana a wasu sassa na titin. Wannan hali ya sa motsin ababen hawa ya ragu musamman a yankin Katari zuwa Jere.

A dalilin haka ne FRSC ta shawarci matafiya su yi amfani da wasu hanyoyi, kamar hanyar Kaduna-Kachia-Maraban Kubacha-Jere-Bwari-Dutse Abuja zuwa Abuja ko Kaduna saboda kaurace wa cunkoso.

Ta ce wadannan hanyoyi za su taimaka wajen guje wa cunkoso da rage shi da kuma inganta tafiyar ababen hawa a lokacin bukukuwa.

Hukumar ta kuma bukaci direbobi su ci gaba da bin dokokin hanya, su guji tukin ganganci da satar hannu/hanya, tare da bin umarnin jami'an kula da hanya.