Jami’an tsaro na sirri a Amurka sun tabbatar da mutuwar wani ɗan bindiga da ake zargi ya buɗe wuta kusa da fadar gwamnatin ƙasar, White House, bayan musayar wuta da jami’an tsaro.
Rahotanni sun ce mutumin ya isa wani wurin binciken ababen hawa da ke kusa da fadar kafin ya fara harbi kan jami’an tsaron da ke bakin aiki.
Nan take jami’an tsaron suka mayar da martani, lamarin da ya jikkata wanda ake zargin da kuma wani mutum da ke kusa da wurin.
Daga bisani an kai wanda ake zargin asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Lokacin da harin ya faru, shugaban Amurka, Donald Trump, na cikin fadar White House.