Gwamnatin Ghana ta zaɓi wani kamfanin cikin gida mai suna Engineers & Planners Ltd domin ya karɓi ragamar gudanar da aikin haƙar zinare na Damang daga kamfanin Gold Fields, kamar yadda ministan harkokin ma’adinai na ƙasar ya bayyana a ranar Talata.

Matakin na daga cikin ƙoƙarin da Ghana ke yi na ƙarfafa kamfanonin cikin gida a fannin haƙar ma’adinai, musamman a masana’antar zinare da ƙasar ta shahara da ita.

A bara ne gwamnatin Ghana ta ƙi sabunta lasisin kamfanin Gold Fields mai hedkwata a Johannesburg, inda ta karɓe ikon gudanar da aikin haƙar ma’adinan na Damang, lamarin da ya kawo ƙarshen yarjejeniyar da ta daɗe tana aiki tsakaninsu.

Bayan haka, gwamnatin ta fara nazartar tayin kamfanonin cikin gida domin farfaɗo da aikin haƙar zinaren wanda ake kiyasin darajarsa ta kai dala biliyan ɗaya.

A cikin wata sanarwa, ministan harkokin ma’adinai na Ghana Emmanuel Armah-Kofi Buah ya ce hukumar kula da harkokin haƙar ma’adinai ta ƙulla yarjejeniya da kamfanin Engineers & Planners Ltd domin ci gaba da gudanar da aikin.