Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya kori Firaminista Ousmane Sonko daga muƙaminsa a wani mataki da ya jawo cece-kuce a fagen siyasar ƙasar.
Rahotanni sun bayyana cewa matakin korar ya biyo bayan zazzafar muhawara da aka yi a majalisar dokokin Senegal, inda Firaminista Sonko ya fito fili ya soki salon mulkin shugaban ƙasar.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin rikice-rikicen siyasa a ƙasar, inda masu sa ido ke ganin cewa zai iya ƙara haifar da saɓani a tsakanin manyan jami’an gwamnatin Senegal