Yusuf Tuggar bai samu tikitin takarar gwamnan jihar Bauchi ba.

Ambasada Yusuf Maitama Tuggar bai samu tikitin takarar gwamnan jihar Bauchi ba, a jam’iyyar APC.

Hakan ya biyo bayan kai ruwa rana tsakanin masu ruwa da tsaki na jihar, kafin daga ƙarshe su tabbatar da tsohon gwamnan Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar a matsayin ɗan takarar gwamnan Bauchi na Jam'iyyar APC, a zaɓen 2027.