Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Filato ta cafke wasu mutane shida bisa zargin satar shanu, hada baki wajen aikata laifi da kuma mallakar bindigu ba bisa ka’ida ba.
Arewa Updates ta rawaito cewa, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Bassey Ewah ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da sashen yaki da manyan laifuka na VCRU a Jos.
Ya ce an cafke daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Yahuza Sale bayan wani bidiyo da ya wallafa a Facebook wanda ake zargin yana tayar da hankalin jama’a.
Sanarwar ta ce Yahuza ya amsa cewa yana hada baki da wani Victor Danladi wanda aka fi sani da Boka wajen satar shanu ta amfani da bindigogin AK47 na gida.
Rundunar ta ce ta kwato bindigogi kirar AK47 na gida guda biyu da harsasai da kuma ƙaramar bindigar guda daya yayin binciken.
Kwamishinan ‘yan sandan ya kara da cewa ana ci gaba da bincike kuma da zarar an kammala za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.