Osimhen ya kai ziyara tsohuwar makarantar firamare da ya yi karatu, ya kuma bai wa mai gadi kyautar Naira miliyan 20.
“Shi ne mai gadin makarantar lokacin da nake karatu a nan. Yakan siya min biskit da ice cream lokacin muna yara ƙanana.
Wasu lokutan nakan zo makaranta ban ci komai ba, sai ya ɗauki abincinsa ya ba ni.
Ga sauran ɗalibai shi mai gadi ne kawai, amma a wurina tamkar uba yake gare ni.
Ba zan taɓa mantawa da shi ba.”