An rantsar da tauraron fina-finan Indiyan nan da ya jagoranci jam’iyyarsa wajen lashe zaɓen majalisar dokokin jihar Tamil Nadu a kudancin Indiya, a matsayin babban ministan jihar.
C Joseph Vijay, jagoran jam’iyyar TVK (Tamilaga Vettri Kazhagam), ya sha rantsuwar kama aiki a gaban dubban magoya bayansa a Chennai, babban birnin jihar.
Mista Vijay zai jagoranci gwamnatin haɗaka, wadda jam’iyyarsa ta lashe kujeru 108 a majalisar dokokin jihar.
Jam’iyyarsa ta TVK ta ƙulla ƙawance da wasu jam’iyyun uku domin samun rinjayen kujeru 118 da take buƙata domin kafa gwamnati.