Gwamnatin Jihar Bauchi, ta hannun Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnati ta Jiha (Civil Service Commission), ta gargadi jama’a da su guji karɓar tayin aikin bogi, tana mai jaddada cewa ayyukan gwamnati a jihar ba na sayarwa ba ne.

Wannan gargadi ya biyo bayan cafke wani mutum mai suna Saleem Alhassan, wanda aka fi sani da “Jagaban Ningi,” da rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta yi bisa zargin forgery da wasu laifuka masu alaƙa.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai a ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati na jihar Bauchi, Awwal Waziri, ya fitar a ranar Asabar.

A cewar sanarwar, an kama wanda ake zargi ne saboda bincike kan zargin haɗa baki da ƙirƙira tare da rarraba takardun aikin gwamnati na bogi ga jama’a.

Ya ce cafke wanda ake zargin ya biyo bayan korafe-korafe da ofishin ya gabatar, wanda kuma ya kai ga gurfanar da wasu mutum biyu a baya kan irin wannan laifi.

Waziri ya bayyana cewa masu damfara suna karɓar kuɗi tsakanin ₦500,000 zuwa ₦750,000 daga hannun jama’a da sunan samar musu aikin gwamnati.

Ya jaddada cewa dukkan daukar ma’aikata a gwamnatin Bauchi na bin tsayayyen tsari ne, kuma ana sanar da jama’a ne ta hanyoyin hukuma kawai.

A cewarsa, babu wani mataki da ake buƙatar biyan kuɗi a lokacin daukar aiki, kuma duk wata takardar aiki da ba ta fito daga ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati ko Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnati ba, karya ce kuma ba ta da inganci.

Waziri ya shawarci jama’a da su guji hulɗa da masu neman kuɗi da sunan samar da aiki, tare da kai rahoto ga ‘yan sanda ko ofishin da abin ya shafa idan sun ci karo da irin wannan hali.

Ya kuma yaba wa rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi bisa gaggawar daukar mataki, tare da jinjinawa sauran hukumomin tsaro kan goyon bayan da suke bayarwa wajen kare tsarin aikin gwamnati.

Gwamnatin ta kuma shawarci duk wanda ke da tambaya kan harkar aiki da ya tuntubi ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati na jihar Bauchi domin tabbatar da sahihancin duk wata takardar aiki.