Gwamnatin Jihar Kwara ta kara kaimi wajen inganta harkar kiwon lafiya matakin farko ta hanyar farfado da cibiyoyin Primary Health Care (PHC) 100 tare da daukar fiye da ma’aikatan lafiya 1,000 a fadin jihar.
Babbar Sakatariyar Hukumar Kula da Cibiyoyin Kiwon Lafiya na Matakin Farko ta jihar Kwara, Nusirat Elelu, ta bayyana hakan a wani taron tattaunawa da al’umma da aka gudanar a Ilorin, inda aka samu halartar masu ruwa da tsaki daga kananan hukumomi 16 na jihar.
A cewar wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar daga Kakakin hukumar, Bukola Abdulganiyu, an shirya taron ne domin karfafa hadin kai tsakanin gwamnati da al’umma kan harkar lafiya.
Elelu ta ce gwamnatin jihar ta dauki matakin farfado da cibiyoyin ne domin tabbatar da cewa kowa na samun ingantaccen kiwon lafiya a matakin tushe.
Ta ce an gyara tare da farfado da cibiyoyin PHC guda 100 a fadin kananan hukumomi 16 domin kusantar da kiwon lafiya ga jama’a.
A cewarta, an tsara aikin ne domin tabbatar da cewa kowace cibiyar lafiya ta zama wurin farko da jama’a ke samun kulawar lafiya, tare da tabbatar da cewa babu wata al’umma da aka bari a baya.
Ta kuma bayyana cewa an gyara cibiyoyi da dama da suka dade a rufe, sannan an samar musu da ma’aikata da kayan aiki domin inganta aiki.
Haka kuma ta kara da cewa gwamnatin jihar ta dauki fiye da ma’aikatan lafiya 1,000 ciki har da likitoci, ma’aikatan jinya da ungozoma domin karfafa aiki a cibiyoyin da aka farfado da su.
A cewarta, taron tattaunawar da aka gudanar an shirya shi ne domin karfafa shigar jama’a cikin harkar lafiya ta hanyar karbar ra’ayoyi, wayar da kai da kuma hadin kai tsakanin gwamnati da al’umma.
A nasa jawabin, jami’in Hukumar Kiwon Lafiya ta Matakin Farko ta Kasa, Hadiza Agbab-Ajao, ta ce shirin na da nufin samar da tsarin kiwon lafiya mai amsawa da kuma mai mayar da hankali ga bukatun al’umma.
Ta ce taron kuma zai taimaka wajen kara fahimtar jama’a kan lafiya, tare da inganta amfani da cibiyoyin lafiya musamman a bangaren mata masu juna biyu, rigakafi, kula da yara da kuma tsarin iyali.
Wani muhimmin bangare na taron shi ne karrama “zakarun PHC” guda bakwai da za su taimaka wajen wayar da kan jama’a kan amfani da cibiyoyin lafiya da aka inganta.
Ko’odinetan hukumar a Kwara, Amina Bello, ta yabawa kokarin gwamnati da abokan hulda wajen inganta kiwon lafiya a jihar.
Ta kuma bukaci jama’a da su rika amfani da cibiyoyin lafiya da ke kusa da su.
Daraktan tsarin kiwon lafiya na hukumar, Michael Oguntoye, ya bayyana cibiyoyin PHC a matsayin wurin farko da ya kamata jama’a su fara neman kulawar lafiya.
Ya ce aikin farfado da cibiyoyin ya samu goyon bayan gwamnati da abokan hulda, kuma an samar musu da wutar lantarki da ruwan sha domin inganta aiki.
Wakilin UNICEF a Kwara, Usman Danlami, ya yaba da kokarin gwamnati wajen inganta kiwon lafiya, yana mai cewa hadin gwiwa da UNICEF na ci gaba da kawo sauki ga jama’a.
Ya kuma tabbatar da cewa UNICEF za ta ci gaba da tallafawa jihar wajen inganta kiwon lafiya mai dorewa da kuma mai hada kowa da kowa.