Rundunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da nasarar kama waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban harsu 248 a cikin wata guda, waɗanda suka kunshi ƴan fashi da makami da masu garkuwa da mutane da masu safarar miyagun kwayoyi da ƴan daba da dai sauransu.
Kwamishinan ƴansandan jihar CP Ibrahim Adamu Bakori ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke gabatar da waɗanda ake a shalkwatar rundunar dake Kano.
Ya ce a lokacin wannan aiki da suka gudanar daga 20 ga watan Afrilu zuwa 20 ga Mayu, sun samu nasarar kama ƴan fashi da makani 18 da masu garkuwa da mutane 5 da masu safarar miyagun kwayoyi 32 da ɓarayin mota 12 dana adai-daita sahu 11 da sai kuma ƴan daba 149.