Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta lalata jabun kayayyaki, magungunan da wa’adin su ya ƙare da kuma marasa inganci da darajarsu ta haura naira biliyan 1.8 a birnin tarayya Abuja.


An gudanar da aikin lalata kayayyakin ne a ƙaramar hukumar Kuje, inda aka ƙone magunguna, kayan abinci, kayan kwalliya, sinadarai, na’urorin lafiya da barasa da hukumar ta kwace daga hannun masu sayarwa da masu safararsu.


Babbar Daraktar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayyana yaɗuwar jabun kayayyaki a matsayin barazana ga tsaron ƙasa. 


NAFDAC ta bayyana cewa masu jabun kaya sun ƙara amfani da dabaru na zamani wajen kwaikwayon kayayyaki na asali, lamarin da ke sa wahalar bambance na gaske da na jabu. 

Hukumar ta kuma yi zargin cewa wasu ƙungiyoyin ƙasashen waje na amfani da raunin tsarin shigo da kaya a Najeriya wajen safarar jabun kayayyaki.