Gwamnatin jihar Anambra ta bayyana cewa tana kokarin bunƙasa noma ta hanyar sarrafa amfanin gona a matakin masana’antu domin bai wa manoma damar samun kuɗaɗen ƙasashen waje ta hanyar noma na kasuwanci da fitar da kayayyaki zuwa waje.
Kwamishinan Noma na jihar, Ben Odoemena, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da kamfanin sarrafa amfanin gona na Ideal Agro Allied Produce Limited da ke yankin Akwaeze a ƙaramar hukumar Anaocha.
Kamfanin, zai riƙa sarrafa doya, rogo, dankali da sauran nau’o’in amfanin gona domin fitar da su zuwa ƙasashen waje.
Odoemena ya ce gwamnatin Gwamna Chukwuma Soludo za ta fi mayar da hankali kan noma na kasuwanci maimakon noma don amfanin gida kawai, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen wadatar abinci da kuma samar wa manoma kuɗaɗen shiga daga ƙasashen waje.