Wani hatsarin mota da ya afku a yankin Sabuwar Mil Uku da ke kan titin Gombe zuwa Yola ya yi sanadin mutuwar mutane biyu, ciki har da wata jami’ar ’yan sanda, yayin da wasu da dama suka samu ji manyan raunuka.
Lamarin ya faru a ranar Laraba lokacin da wata tirela ƙirar DAF mai ɗauke da buhunan hatsi ta kwacewa direban ta, inda ta kutsa cikin babura uku da masu tafiya a ƙasa tare da wasu shaguna da ke bakin hanya.
Rahotannin farko daga jami’an tsaro sun nuna cewa direban motar ya yi ƙoƙarin kutsawa hanyar da ba ta dace ya shiga ba, sannan birkin motar ya gaza aiki, lamarin da ya haddasa hatsarin.
Wata jami’ar ’yan sanda mai suna Sharifa Gaina ta rasu nan take a wurin, sannan wani mutum da ba a tantance sunan sa ba shima ya rasa ransa sakamakon hatsarin.
Sauran mutanen da suka jikkata, ciki har da direban tirelar, an garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Gombe, Umar Ahmed Chuso, ya jajanta wa iyalan mamatan tare da kira ga direbobi su riƙa kiyaye dokokin hanya da kuma tabbatar da lafiyar motocin su kafin tafiye-tafiye.
Shi ma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu tare da addu’ar Allah Ya jikansu.