Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya janye daga takarar neman tikitin tazarcen kujerar Gwamna da yake a kai a APC wanda aka shirya gudanarwa ranar Alhamis.
A cikin wata sanarwa mai taken “My Decision to Withdraw from the Rivers State Gubernatorial Primaries”,da jaridar Daily Trust ta gani, wadda ya sanya wa hannu da kansa a daren Laraba, Fubara ya bayyana cewa zai mara wa duk wanda ya fito a matsayin dan takarar jam’iyyar APC baya.