Ƙungiyar Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), wadda ke da alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda a yankin Sahel, ta yi ikirarin kashe wani soja a wani hari da ta kai kan sansanin sojoji a arewacin Benin.
Wannan shi ne karo na farko cikin watanni da ƙungiyar ta yi ikirarin kai hari a Benin.
JNIM ta fitar da sanarwar ikirarin ne ta kafar yaɗa labaranta ta al-Zallaqa, a tasharta ta ChirpWire, a ranar 10 ga Satumba.
A cikin sanarwar, ƙungiyar ta ce a ranar 9 ga Satumba ta kai hari kan wani sansanin sojoji da ke ƙauyen Kantoro, kusa da garin Guene, a sashen Alibori.
Ƙungiyar ta ce harin ya yi sanadin mutuwar wani soja.
Wannan shi ne harin farko da JNIM ta yi ikirarin kai wa a Benin tun bayan wasu hare-haren da aka danganta da ita a watan Mayu.
Yawancin hare-haren ƙungiyar a Benin na faruwa ne a yankunan arewacin ƙasar, musamman wuraren da ke kusa da iyakar Benin da Nijar.
Sai dai har yanzu ba a samu cikakken bayani daga hukumomin Benin kan harin da kuma ikirarin JNIM ba.