Mahukunta a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo sun tabbatar da mutuwar yara ƴan makaranta aƙalla 24 sakamakon wata mummunar gobara da ta tashi a wasu makarantu biyu a birnin Bukavu da ke gabashin ƙasar.

Lamarin ya janyo ruɗani sosai, yayin da aka samu rahoton mutuwar wasu manya tare da jikkatar mutane da dama da aka garzaya da su asibitoci domin samun kulawa.

Rahotanni sun ce gobarar ta kuma lalata gidaje kusan 300, yayin da har yanzu hukumomi ba su gano musabbabin tashin wutar ba.

Hotunan da aka yaɗa a kafafen sada zumunta sun nuna ƙananan yara kwance a asibiti, wasu na fama da raunukan ƙunar wuta, yayin da wasu hotunan ke nuna yara kwance a ƙasa.

Shaidun gani da ido da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya zanta da su sun ce an shawo kan gobarar tun da rana, amma har yanzu ana ganin hayaƙi na fitowa daga ƙarƙashin wasu gine-ginen da aka rusa domin dakile sake yaɗuwar wutar.

Bukavu, wanda ke cikin yankin Kivu, na daga cikin wuraren da suka fi fama da cunkoson jama'a a gabashin ƙasar. Birnin ya faɗa ƙarƙashin ikon mayaƙan ƙungiyar M23 a watan Fabrairun 2025.

Bayanan da hukumomin da ke iko da birnin suka fitar sun ce adadin waɗanda suka mutu ya kai 24, amma ana fargabar cewa adadin na iya ƙaruwa saboda wasu daga cikin waɗanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.

A nata ɓangaren, gwamnatin ƙasar da ke Kinshasa ta bayyana damuwa matuƙa kan lamarin, ko da yake ba ta bayyana adadin mutanen da suka mutu ba.

Ma'aikatar Ilimi ta ce an samu asarar rayuka da dama tare da jikkatar wasu, inda ta miƙa ta'aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Ta kuma bayar da umarnin gudanar da bincike kan makarantun da abin ya shafa tare da daukar matakan da za su ba da damar ci gaba da harkokin karatu.

Wannan gobara ta faru ne kwanaki kaɗan bayan wata gobara da ta tashi a Kinshasa, babban birnin ƙasar, inda aka samu asarar rayuka yayin da mutane ke ƙoƙarin tserewa daga wata gobara da ta tashi a wajen wani ɗakin taro yayin da ake gudanar da biki.

Bayan waɗannan abubuwan, gwamnatin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ta umarci hukumomi da su ƙara tsaurara matakan kariya daga gobara tare da sanya ido sosai a wuraren da ake taruwar jama'a.