Majalisar Dokokin Najeriya ta dakatar da duk wasu ziyarce-ziyarcen aiki da jami’an majalisar ke yi zuwa Afirka ta Kudu, biyo bayan rahotannin hare-haren ƙyamar baƙi da ake zargin ana kai wa ’yan Najeriya da sauran ’yan Afirka a ƙasar.

Majalisar ta kuma ce za ta kaurace wa duk wasu ayyukan majalisa da za a gudanar a Afirka ta Kudu har zuwa wani lokaci.

A cikin wata sanarwa, Magatakardar Majalisar Dokokin Najeriya, Kamoru Ogunlana, ya bayyana cewa majalisar na matuƙar damuwa kan rahotannin kashewa, raunatawa da kuma raba ’yan Najeriya da muhallansu, tare da tilasta wa wasu barin sana’o’i, gidaje da kadarorinsu.

Majalisar ta buƙaci gwamnatin Afirka ta Kudu ta ɗauki matakan kare baƙin da ke zaune a ƙasar, tare da gudanar da cikakken bincike kan hare-haren da aka ruwaito da kuma gurfanar da duk waɗanda aka samu da hannu a cikinsu.

Rahotannin tashin hankalin sun ƙara janyo damuwar Najeriya kan tsaron ’yan ƙasarta a Afirka ta Kudu. A watan Yuni, Najeriya ta fara shirya kwashe wasu daga cikin ’yan ƙasarta daga ƙasar saboda fargabar tsaro.

A cewar gwamnatin Najeriya, sama da ’yan Najeriya 1,500 ne suka dawo gida tun daga lokacin, yayin da wasu ƙasashen Afirka ma suka ɗauki matakai na taimaka wa ’yan ƙasarsu barin Afirka ta Kudu.

Sai dai Majalisar Dokokin Najeriya ta jaddada cewa matakin ba yana nufin Najeriya ta yanke hulɗar diflomasiyya da Afirka ta Kudu ba, illa dai nuna damuwa da kuma matsin lamba kan hukumomin ƙasar su tabbatar da tsaron ’yan Najeriya da sauran baƙi.

Hukumomin Afirka ta Kudu sun musanta wasu daga cikin zarge-zargen, tare da cewa ana gudanar da bincike kan abubuwan da aka ruwaito.