Mayakan Houthi sun ƙwace iko da tsibirin Zaqr (Zuqar) da ke kudancin Tekun Bahar Maliya, a wani sabon mataki da ke ƙara ƙarfafa ikonsu a yankin mashigar ruwa ta Bab al-Mandab.

Rahoton kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce mayaƙan sun kai farmakin ne ta hanyar amfani da rokoki da kuma kwale-kwalen da ke ɗauke da mayaƙa.

A ranar Alhamis kuma, shaidu sun ce mayaƙan Houthi sun shiga birnin tashar jiragen ruwa na Mokha (Mocha), suna rera taken “Mutuwa ga Amurka, mutuwa ga Isra’ila.” Wata majiya ta soji ta tabbatar wa AFP cewa Houthis sun ƙwace birnin, wanda ke da muhimmiyar matsayi saboda kusancinsa da mashigar Bab al-Mandab.

Mokha na daga cikin muhimman wuraren da ke gabar Tekun Bahar Maliya, kuma kwace shi na bai wa Houthi damar ƙara matsa kusa da Bab al-Mandab, ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar kayayyaki da makamashi a duniya.

AFP ta ce yaƙin da ake yi a Yemen tun bayan fara sabon farmakin Houthi a makon da ya gabata ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 500, galibinsu mayaƙa.

Haka kuma, Ƙungiyar Kula da Ƙaura ta Duniya (IOM) ta ce kusan mutum 20,000 sun bar gidajensu sakamakon faɗan da ake yi a yankunan da ke kusa da gabar Bahar Maliya.

Ƙwace Mokha da ci gaban Houthi zuwa tsibiran Hanish na ƙara tayar da fargabar cewa rikicin zai iya sake rikidewa zuwa babban yaƙi, tare da ƙara barazana ga zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Bab al-Mandab.